29 Yuni 2021 - 11:11
Majalisar Dokokin Kasar Rasha Ta Bukaci A Tattauna Batun Hare-Haren Da Amurka Ta Kai Kan Iyakar Kasashen Siriya Da Iraki A Gaban Kwamitin Tsaro Na MDD

Shugaban kwamitin al-amuran harkokin waje, a majalisar dokokin kasar Rasha a Moscow, (DUMA) Leond Slutsky ya bukaci kwamitin tsaro na MDD ya tattauna batun hare-hare na baya-bayan nan, wanda jiragen yakin Amurka suka kai a kan iyakar kasar Syriya da Iraki.

ABNA24 : Kamfanin dillancin labaran SANA na kasar Siriya ya nakalto Slutsky ya na fadar haka a yau Talata a birnin Mosco. Ya kuma bayyana hare-haren na Amurka a matsayin dabbanci.

Har’ila yau Slutsky ya yi kakkausar suka kan kudurin da kasashen yamma suka gabatar don tsawaita abinda suka kira shirin bada agaji na gwamnatin kasar Amurka, ga mutanen kasar Siriya, inda take ruwam boma-bomai a kansu a bangaren guda sannan a wani bangaren kuma wai ta na basu agaji.

342/